Labaran Yau

Wani Ya Kashe Abokin Sa Garin Gwada Maganin Bindiga

Rahotanni sun bayyana cewa wani mutum mai suna Bode ya gudu bayan ya kashe wani mai suna Tunde Akinmoyewa da bindiga a kauyen Laoso da ke karamar hukumar Ondo ta Yamma a jihar.

Wata majiya ta shaida wa jaridar Punch cewa, abokin nasa ne ya harbe tsohon mai laifin mai shekaru 27 a duniya yayin da yake gwada wata sabuwar bindiga da aka kera a cikin gida a ranar Talatar da ta gabata.

“Don gwada ingancin layar da ya karba ta maganin bindiga, Tunde ya nemi abokinsa (Bode) da ya fara harbin. Bayan abokin Tunde ya dauko bindiga ya gwada harbin shi (Tunde), kwatsam sai ya Tunde ya fadi ya mutu nan take.

“Da ya ga abin da ya faru, wanda ake zargin ya bi duhu kafin makwabta su je wurin faruwar abun kuma ba a kama shi ba.”

An garzaya da marigayin asibiti mafi kusa da kauyen, inda aka tabbatar da rasuwarsa. Kakakin rundunar ‘yan sandan Ondo, Funmilayo Odunlami, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce sun fara gudanar da bincike kan lamarin.
Odunlami ya ce;
“Wani mai suna Tunde Akinmoyewa, wanda aka yankewa hukuncin daurin rai da rai, wanda kuma dan kungiyar asiri ne, a lokacin da yake gwada wata bindigar da aka kera a cikin gida da ake kyautata zaton ya saya, yayi amfani da ita gurin gwajin maganin bindiga akan yaronsa mai suna Bode, wanda har yanzu ba a san sunan sa na asali ba, ya harbe shi, a dalilin haka ya mutu a lokacin da ake tsare da shi. an kai shi asibiti domin kula da lafiyarsa.
“A halin da ake ciki, an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa yayin da ake kokarin kama wanda ake zargin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button