Labaran Yau

Zulum Ya Bude Sabbin Gidaje 200 A Karamar Hukumar..

Zulum ya bude sabbin gidaje 200 a karamar hukumar Nganzai

Gwamnan jihar borno, Farfesa Babagana Umara Zullum, ya bude sabbin gidaje da gwamnatin tarayya ta gina guda dari biyu a Gajiram dake kamar Hukumar Nganzai a jihar borno.

A yayin bude gidajen, Zulum yace wannan cigaba ne wanda Shugaba buhari ya kawo a karkashin aikin SDGs.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Yace aikin anyi ne dan samawa wanda suka rasa muhalli suke gudun hijira, bayan abubuwa da suka faru a baya a jihar.

Sama wa mutane muhalli shine mataki na farko dan bawa mutane yan ci gyara na rayuwa, wa mutanen da ta’addanci ya bata wa rayuwa.

“Hakan zai bada nutsuwa na fuskantar rayuwa da Kuma lura wajen tsaro da kuma yalwantuwar rayuwa” a cewar sa.

Shi gwamna ya yabi Shugaban kasa da ofishin SDG wajen gina gidajen wa mutanen gajiram.

Yq bayyana hazaka da suka sa dan dawowan mutane gida da gyaran wuraren su bayan matsalolin da suka fuskanta na ta’addanci.

Mai taimakawa Shugaban kasa akan SDG, Adejoke Adefulire, ta yaba wa zulum wajen taimakawa da yayi akan aikin dan cimma nasaran aikin.

Ta ce Shugaban kasan Najeriya yana kaunar ya ga an dakile rashin zaman lafiya da Kuma gyaran gidajen da aka bata da ta’addanci.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button