Labaran Yau

Tinubu Yasa Ayi Farautan Makisa a Jihar Filato Da Benue

Tinubu Yasa Ayi Farautan Makisa a Jihar Filato Da Benue

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya saka jami’an tsaro dasu nemo masu haddasa kashe kashe a karamar hukumar Mangu na Jihar Filato da wasu yankin jihar Benue.

Shugaban kasan ya yi jawabi wanda ya fito ya bakin daraktan Shugaban kasa kan zantarwa Dele Alake, ya bayyana rashin jin dadi a bayyane kan kashe kashen da akeyi.

Tinubu ya nuna fushi da jimami akan tashin hankalin da aka samu a Jihar Filato, yace farmaki da ake kaiwa da kashe kashe da kona gidaje na jihohi biyu abu ne mai rashin dadin ji.

Ya Kuma jaddada wa Jihar Filato da Benue da kuma Hukumar bada dauki da su yi kokari wurin bada goyon baya da dauki wa wanda musiban ta shafa suka rasa gidajen su.

Ya nuna matsayin gwamnatin shi wajen kokarin dakile Duk wani harka ta tashin hankali da sauran laifuffuka da  ta’addanci a duk sassan kasar Najeriya.

Shugaban kasa Tinubu yana kiran Shugabanin gargajiya da masu anguwanni, kungiyoyi da Kuma Shugabancin Arewa consultative Forum, jama’a tul Nasrul Islam, Christian Association of Nigeria da su hada kai suyi aiki tare domin gina zaman lafiya, yarda da juna dan kawo zaman lafiya a wannan wurare da tashin hankalin ya shafa.

“Abin da ya fi kona rai gaba daya a cikin wannan yaki shine, Yar wata takwas a farin Lamba na garin Vwang a karamar hukumar Jos ta kudu, ta rasu a tashin hankalin wanda bata ji ba bata gani ba”

“Manyan abubuwan da suke zuwa su dawo akan Tashin hankali shine rasa rayukan wanda basu da hurumi ciki, domin samun kwanciyan hankali da cigaba Sai an samu yafiya da zamantakewa Mai daurewa”

Shugaban kasan ya bayyana a Jawabin sa mai suna kisan filato, Sai Mun balla zagayen kashe kashe.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button