Labaran Yau

Laporta Ya Zanta Da Manema Labarai

Laporta Ya Zanta Da Manema Labarai

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake andalus ya zanta da jaridar mundo deportivo da yammacin ranar talatar nan.

Anyi masa tambaya akan shahararren Dan wasan gaba na Argentina wato Leo Messi inda yace “muna da alaqa mai dadi tsakaninmu da leonel Messi amma bamuyi magana dashi ba bayan matakin daya dauka da rattaba hannu a kungiyar inter miami dake amurka, amma muna masa fatan nasara, mun shirya masa kwantaragi amma bazai yiwu mu cigaba ba saboda wasu ka’idoji amma Barcelona zai cigaba da zama gidansa”.

Akan sababun yan wasa, shugaban yace “Muna bukatar dan bayan guda da kuma yan kwallon tsakiya biyu shikenan kungiyarmu ta cika kamar yadda mai horaswa xavi ya nema”.

Laporta Ya Zanta Da Manema Labarai
Laporta Ya Zanta Da Manema Labarai

Akan kwantaragin mai horaswa xavi “Yace zamuyi a lokacin da ya dace idan mun kammala daukan yan wasanmu”.

Anyi wa shugaban tambaya akan makomar dembele da ansu fati inda yace dukkan yan wasan suna son kungiyar kuma kungiyar kwallon tana sonsu, Dan haka zasu cigaba da zama a kungiyar.

Anyi masa tambaya kuma akan arder guler daya koma Madrid daga Fernabace shugaban yace sun cimma yarjejeniya ta cinikayya sai kungiyar kwallon kafa ta real Madrid ta kara kudi Dan haka ba zamuyi gasa dasu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button