Jami’an yan sanda sun samu nasaran damke Mutum dari bakwai da Tamanin da daya(781) suke kulle akan hargitsi da badakalan zaben da ta gabata
Yan sandan Najeriya sun ce a shirye suke suyi aiki don kame da ladabtar da Duk wanda aka samu hanun shi cikin hargitsi da badakala wajen zabe, a zaben da ta gabata a Najeriya gaba daya.
Inspeto janar din yan sanda, Usman Baba, yayi magana da manyan jami’an yan sanda jiya a babban ofishinsu dake Abuja.
Ya ja musu kunne da Kuma su jajirce wajen aiki tare da jamian Zabe INEC domin hunkunta Duk wanda aka kama da hannu a domin bata sakamakon zaben da ta gabata.
A cikin bayanin sa ya yaba yan sandan wajen ayyukan da sukayi wajen kame daga dari biyu da takwas (208) na zaben shugaban kasa zuwa dari bakwai da tamanin da daya (781) a zaben da akayi na gwamnoni da yan majalisu.
Insipeto janar Usman ya jaddada dacewa jamian yan sanda su kara kwazo wajen dakile Duk wata tarzoma ta zata faru nan gaba dan samun tsaro wa qasa baki daya.
Daga Bisani Na Labaran Zaben Bauchi Wani Matashi Da Aka Sanida Masoyi Lamba Daya Na Meh Girma Gwamna A Jahar Bauchi Mai Suna “Jamil Na Kaura ” Ya Jagoranci Murnar Cin Zaben KAURAN BAUCHI Karo na Biyu a yanar sada zumunta na fezbuk