
Hukumar Raya Shiyar Arewa Maso Gabas, North East Development Commission, ta bude shafin yanar gizonta, domin daukan matasa maza da mata, wadanda za’a koya musu sana’a. Bayan an koyar da sana’ar Kuma, za’a tallafa musu da kayan sana’ar.
Hukumar ta saba yin wannan lokaci zuwa lokaci. Wannan karon za su koyar da sana’o’in gyaran handset ne da kafa na’urar sattelite, amma wa matasan da ke zaune a Shiyar Arewa Maso Gabas, wato, Jihohin Bauchi, Gombe, Yobe, Borno, Adamawa da Taraba.
Matasa mazauna wadannan jihohin, sai a hanzarta a nema.
Ga link din da zakayi Register:
https://admin.nedcresourcecentre.org/register