NEWSLabaran Yau

Qasar Da Aka Hana Kiran Sallah Da Lasfika A Afrika Maso Gabas

Qasar Da Aka Hana Kiran Sallah Da Lasfika A Afrika Maso Gabas

Hukumomin dake qasar Rwanda sun titsiye yin amfani da lasifika wajen kiran Sallah a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, saboda ta rage abin da suka kira ‘hayaniya ga muhalli’.

Hukumomin sun zantar cewa shi kiran sallah a masallatan da lasifika ya saba dokar nan da ta hana hayaniya a cikin jama’a.

Gwamnatin kasar dai ta ce sai dai Musulman kasar su saita kararrawar waya daidai lokutan sallolin idan suna son su tuna lokacin sallah. Sai dai wasu musulmin kasar na zargin cewa an tauye musu ’yancin yin addini, la’akari da cewa ba dukkan Musulman ba ne suka mallaki wayar salula.

Ita gwamnatin Rwanda dai ita ce ta inganta birnin na Kigali din ya zama daya daga cikin manyan birane a Afirka a bangaren zuba jari da yawon bude ido nan da shekaru 22 masu zuwa. Musulman birnin dai tuni suka fara bin umarnin, kodayake sun soki lamirinsa, inda suka ce kamata ya yi a ce su rage sautinsu a maimakon haka.

Sai dai abin dubawa anan shine matakin ba bawai ya tsaya iya masallatai kawai bane, saboda ko a watan da ya gabata sai da aka rufe coci-coci kusan 700, saboda saba wa umarnin da Gwamnatin ta wanzar a qasan.

Domin Sammun Sabbin Labarai Danna ⇒ Sabbin Labarai

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button