Labaran YauNEWS

Saura Qiris Yen Bindiga Su Rasa Maboya – Shugaban NAF

Saura Qiris Yen Bindiga Su Rasa Maboya – Shugaban NAF

Babban hafsan sojin sama (CAS), Air Marshal Oladayo Amao ya sha alwashin cewa, yen  bindiga ba za su samu wurin buya ba a kasar nan cikin wata guda mai zuwa.

Amao ya bayyana hakan ne yayin ziyarar gwamnan jihar Katsina, Honarabul Aminu Bello Masari zuwa Ofishin Shugaban sojin saman a Abuja.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Masari ya yaba wa Sojojin saman Nijeriya (NAF) saboda yadda suka nuna kwazo a yaki da ‘yan bindiga da sauran nau’ikan aikata laifuka a Katsina da wasu jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Ya kuma kara da cewa, jajircewa da sadaukarwar da Shugaban sojojin sama (CAS), Air Marshal Oladayo Amao, da kuma kokarin da jami’an NAF ke yi a kan gaba a ayyukan ci gaba a yankin Arewa maso Gabas ya takaita ayyukan yen ta’adda kuma suna iyakance yanayin aikinsu.

Da yake ci gaba da magana, gwamnan ya bayyana cewa, ta’addanci a jihar ta Katsina da kewayenta wani sabon abu ne saboda ba ya wakiltar kowace irin akida, addini ko jam’iyyar siyasa.

A cewarsa,  yen


bindiga a Katsina ta’addanci ne kawai.”

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar Katsina ta yi kokari sosai wajen fatattakar ‘yan ta’addan, amma motsawar ba ta da wani sakamako ko kadan sakamakon kowace kungiya na gudanar da ayyukanta na kashin kansu.

Matsalar tsaro, a cewar gwamnan, ta haifar da fadada kan iyakar Katsina da Jamhuriyar Nijar da kuma manyan wuraren da ba a iya gudanar da su a cikin jihar, wanda ke bai wa ‘yan bindigar ‘yancin motsi.

Ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ayyukan bata gari, wadanda suke da nasaba da lalata rayuka da dukiyoyi, satar mutane, fyade da kone-kone ya yi matukar tasiri ga ci gaban jihar.

Abin da ya fi tayar da hankali, a cewar gwamnan, abin takaicin shi ne yadda wadannan ‘yan bindiga ke kai hari a yankin da suke zaune da kuma mutanen da suka zauna tare shekara da shekaru.

Duk da yake lura da cewa za a iya jin fifikon shugabanci ne kawai lokacin da aka samu zaman lafiya da tsaro. Gwamna Masari ya bayyana cewa, dole ne a yi duk mai yiwuwa domin kawar da barayin mutane don dawo da martaba da daidaito a duk yankin Arewa maso yammacin Nijeriya.

Ya nuna farin cikinsa da irin hadin kan da ke tsakanin hukumomin tsaro daban-daban sannan ya bayyana cewa, sakamakon sabon matakin hadin gwiwar ya fara samar da kyakkyawan sakamako tare da ganin ana samun wasu matakan na yau da kullum a wasu yankunan jihar.

Don haka ya yi kira ga hadin kan ‘yan Nijeriya yayin da sojoji ke aiki ba dare ba rana don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi.

Da yake amsawa,Shugaban sojin ya yaba wa Masari saboda goyon bayan da yake bai wa NAF da sauran hukumomin tsaro a jihar Katsina.

Ya kuma sanar da gwamnan kan samun cikakken goyon baya daga NAF a matsayinsa na ba sulhu da ‘yan bindiga, yayin da ya ba shi tabbacin cewa ba da wani lokaci mai tsawo ba, yanayin tsaro zai juya zuwa mafi kyau.

Air Marshal Oladayo ya kuma yi amfani da damar ziyarar don sanar da gwamnan cewa dokar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shugabannin tsaro a bayyane take kuma ba tare da wata shakka ba Shugaban kasar ya ce, “Ku yi maganin dukkan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a kasar.”

A cewar Shugaban sojin saman, “tare da shigar da sabbin dandamalin jirage ciki har da ‘Super Tucanos’ da sauran dandamali, a cikin wata daya zuwa biyu masu zuwa, ba za a samu wurin buya ga wadannan ‘yan bindiga ba.”

Dangane da ayyukan NAF da ke gudana a jihar Katsina, Air Marshal Amao ya ba Gwamna Masari tabbacin cewa idan aka kammala su, ayyukan za su bunkasa karfin aiki da kuma isa ga dandamali na NAF a jihar.

Jawabin ziyarar ya hada da sanya fure a filin wasan tunawa da NAF game da jami’an NAF wadanda suka rasa rayukansu a yayin gudanar da aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button