Labaran YauNEWS

Yen Bindiga Sun Sace Wasu Tare Da Harbe Shugaban Miyetti Reshen Abuja

Yen Bindiga Sun Harbe Shugaban Miyetti Reshen Abuja

Yen Bindiga sun harbe shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa reshen karamar hukumar Gwagwalada dake garin Abuja, Alhaji Adamu Aliyu.

Sakataren Kungiyar Mohammed Usman ne ya tabbatar da faruwar hakan a yau Lahadi, inda ya kara da cewa, an kashe shi ne tare da wasu mutane hudu a daura da kauyen Daku da ke a mazabar Dobi a ranar Alhamis da ta gabata.

Ya ce,  Yen bindigar sun kuma sace mutum uku, inda uku su ka samu raunuka saboda harbin ‘yan bindigar wadanda a yanzu, suna a wani Asibitin Abuja, ana yi masu magani.

Usman ya ce, lamarin ya auku ne daidai lokacin da Adamu ke a kan hanyar sa ta dawowa gida daga kasuwar Izom ta jihar Neja bayan ya je sayar da shanu tare da sauran wadanda lamarin ya rutsa da su.

Shugaban karamar hukumar Gwagwalada Adamu Mustapha, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button