Labaran YauNEWS

Kisan Fatima Da Yaranta – Bazamu Lamunci Kisan Da Ake Yiwa Yan Arewa A Kudancin Najeriya Cewar Kungiyar Matasa

Bazamu Lamunci Kisan Da Ake Yiwa Yan Arewa A Kudancin Najeriya Cewar Matasan Arewa

Abubuwan da suke faruwa sunyi yawa wanda har kungiyar matasan Arewacin Nigeria da aka sani Northern Yourth Coucil of Nigeria (NYCN), ta yi kira ga gwamno nin Kudancin kasar da manyan shuwagabanni kan su yi kokarin kawo karshen kisan kiyashin da ake yiwa yan Arewa mazauna yankin Kudu.

Maganan matasan ya fitone ta hannun shi shugaban kungiyar ta (Northern Yourth Coucil of Nigeria) a ranar Talata a jihar Kaduna.

Kiran yana zuwa ne bayan da aka sami manbobin tsagerun masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB) suka kashe wata mata mai suna Harira Jibril da yaran ta su hudu a jihar Anambara.

“Mutanan mu na Arewa ya zama dole abasu damar su da suke da ita na zagayawa ko’ina a fadin Nigeria, dan haka muna jan kunanasu kashe mana mutanen Da sukeyi su saurara da zubar da jinin mu haka domin a zauna lafiya guri daya” acewar kungiyar.

Inda suka kara da cewa

” muna kira ga dukkan bangarorin hukumomin tsaro da su tabbatar sunyi abun da ya kamata game da kisan da ake yi mana bazamu lamunta ba.

Kisan Fatima Da Yaranta Muna Kan Binciken Bidiyon Don Sanin Sahihancinsa Cewar Buhari

Yanzu haka fadar shugaban kasa (Villa) ta gargadi yan Najeriya kan yunkurin mayar da martani bisa bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta na kisan wata mata ‘yar Arewa wanda takeda juna biyu tare da ‘yayanta hudu.

Wanda yake magana da yawun shugaban kasa, mai suna Malam Garba Shehu, a jawabinsa da ya fitar ranar Laraba yace Shugaba Buhari ya kira ga yan Najeriya kada suyi gaggawan hukuncin kan bidiyon.

Domin Samun Sabbin Labarai Cigaba Da Shigowa Shafin Jaridarmu Ta Labaranyau

 

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button