Labaran Yau

Gwamnoni Uku Cikin Gwamnonin Arewa Wanda Sukayi Ruwa Sukayi Tsaki Wanda Zasu Tashi A Tutar Babu Mulkin Tinubu

Gwamnoni Uku Cikin Gwamnonin Arewa Wadanda Sukayi Ruwa Sukayi Tsaki Da Suka Tashi A Tutar Babu

Yanzu haka Jami’inmu na Labaranyau Blog ya samu kishin kishin kan cewar Gwamnoni uku cikin gwamnonin Arewa wadanda sune sukai ruwa sukai tsaki wajen tabbatar da samun nasarar Bola Tunubu alamu ya nuna za a shanye jar miyar amarya su suna kofar gidan ango.

Masana harkokin siyasa sunyi hasashen babu Wani shiri da Gwamnati maici takeyi don ganin Ta Basu wasu manyan mukamai acikin wannan gwamnatin,

Bayanin sirri da muka Samu dai ya nuna aiki aka Basu kuma abinyasu ladan aikinsu tun kafin suyi aikin, sannan wasu na kallon za ai musu irin abinda Bahaushe kecewa ne, ingiza mai kan turuwa.

Ga gwamnonin daga bisani da zasu tashi a tutar babu

1. Abdullahi Umar  Ganduje Tsohon Gwamnan Kano

2. Nasiru El Rufai Tsohon Gwamnan Kaduna

3. Bello Matawalle Tsohon Gwamnan Zamfara

Ki meh zaka iya cewa dangane da wannan abu? Shin abinda Shugaban Kasa Tinubu ke nemanyi daidai neh ko kuma da gyara?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button