Kayan hadi
Zobo (barekata na zobo) Rabin mudu
Abarba guda daya
Cucumber guda uku
Lemo guda uku zuwa biyar
Kanwa Rabin teaspoon
Citta manya 3
Kaninfari cokali daya
Sinamon stick dogo daya
Lemon grass(optional)
Na’a na’a (optional)
Yadda zaki hada
Dafarko zaki wanke abarba guda daya ki bare kisa bawon a tukunya sai ki markada abarban ki tace ruwan sai tuttukan ma kisa a tukunya
Sai kibare bawon lemon ki zubar kicire kwallon lemon ma ki zubar sai ki yayyanka lemon kisa a tukunyan lemo guda hudu
Ki markada cucumber guda uku manya idan kanana ne guda hudu ki tace ruwan kisa a gefe tare da ruwan abarban tuttukan sai ki sashi a tukunyan
Sai a dauraye zobon kar yakai Rabin mudu idan me kyau ne Amma yadan fi quarter idan ba me kyau sosai bane ayi amfani da Rabin mudu Shima asa a tukunya a daka citta,kaninfari da cinnamon asa a wanke ganyen na’a na’a da lemon grass asaka a dafasu na tsawon minti arba’in (40) adan Saka kanwa Dan kadan rabin teaspoon ko baking powder saboda cire tsami idan yayi sai a bari ya huce a tace
Amma de so samu a dafashi da yamma ko da dare abarshi ya kwana washegari a tace Hakan na sashi ya jiku sosai kayan hadin su fito kuma Yana Kara mishi kauri
Bayan an tace sai a zuba ruwan lemo da abarban da aka tace asaka a ciki sa’annan asaka sugar daidai yanda akeso asha.
Idan ana son asaka flavour zaa iya Sakawa Amma barinshi natural din yafi amfani ga lafiya.