Labaran Yau

An Nada Sarki Charles Na Uku A Westminster Abbey Na Garin Landan

An Nada Sarki Charles Na Uku A Westminster Abbey Na Garin Landan

Ranar Asabar, an nada Sarki Charles na uku. babban bikin sarautan da akayi tun shekaru 70 baya, ta samu maimaici inda ka bayyana shafin Al’ada.

A gaban manyan Shugabannin duniya dari da Kuma yan kallon talabijan mutum miliyoyi, Archbishop na Centerbury da Babban Shugaban cocin Anglican.

Aka sanya mai hulas sarauta ta tsohuwar st Edward, Ya kuma zauna akan kujerar sarauta ta karni 14 a Westminster Abbey.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Irin wannan bikin an kamanta ta da wanda akayi shekaru 74 na William the conqueror a shekarar 1066.

Matar charles ta biyu Camila Mai shekara 75 tazama sarauniya a bikin awa biyu. Abinda ya jima bai faru ba a tarihi, hakan ya nuna cewa mulkin cigaba zata kawo, wanda tazo da yawan mutane da suka fito daga wurare daban daban da addinai cikin Al’amarin mulkin.

A kasar da ta ke kokarin samun tsayayyan Shugaban gudanarwa na tattalin arziki da siyasa, da tarzoma bayan fita daga European Union, da kuma kula da matsayin su a idon duniya.

Masoyan masarautar sun bayyana cewa sun nuna girmansu a idon duniya, Kuma sunyi abinda zai sasu su zauna da mutunci a duniya.

“Ba wata kasa da zata iya yin biki irin wanda akayi daga shafin Al’ada, yanda akayi nadin da sauransu” cewar Rishi Sunak.

Duk da Sunak yaso hakan, anyi Nadin sarautar ne cikin tsadan rayuwa. Wanda yasa matasa basu ganin kimar gidan.

Bikin da akayi ranar Asabar kadan ne cikin wanda akayi in an kimanta da na Sarauniya Elizabeth a shekarar 1953, amma a kayace da nuna duniyar gwal da dutsen diamond masu kyau da tsada.

Charles ya gaji sarautar wajen mahaifiyarsa yazama sarki bayan rasuwan ta a watan satumba . Nadin sarautar ba dole bane amma dan jaddada sarautar wa jama’a.

An kai sarki da sarauniya bikin sarautar a Abbey da runduna masu huluna mai kyalli.

Sojoji sun saka kayansu ta biki suka yi tattaki zuwa fadar buckingham. Mutane ko ta Ina, wasu sun tsaya ne a inda zasu iya kallo, dan nisan wurin da yawan mutane. Wasu sunce wannan taron tarihi ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button