Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin Dala miliyan 800 kamin a cire tallafin mai
Gwamnatin tarayyan Najeriya tace ta karbi bashin dala miliyan dari takwas a bankin duniya domin magance wahalan da za a shiga dan neman sauki in an cire tallafin mai a watan Yuni 2023.
Ministan kudi, kasafi da tsare tsare, Zainab Ahmed, ta bayyana a fadar jiha na gwamnati, bayan tattaunawarsu wanda akeyi a kowani mako a Abuja
Malama Zainab tace wannan kudin ya samu Kuma yana shirye dan rabawa, kuma kudin sharar ruwa ne dan kwantar da hankalin Al’umma.
Ta kara da cewa Suna aiki ne tukuru dan samu fita daga tallafin Mai, Sai yasa muka samo kudi a bankin duniya dan tallafawa talakawa da nakasassu, Kuma za a rabawa wanda basu da galiho wanda aka musu rajista a rajistan kula da rayuwa na kasa.
“A yau akwai mahalli miliyan goma, wanda yakai akasarin mutum miliyan hamsin”
Ministan da kara da cewa gwamnati a shirye take dan bada masauki wa cire tallafin Mai dan shiryawa da tayi dan magance wahalhalun da zai iya gabatowa.
Majalisan Dattawa ta bayyana masu daukan nauyin gyaran hanyan jirgin kasa ta Kano-kaduna
Majalisan dattawa ran talata ta bayyana wanda zasu dau nauyin gyaran jirgin kasa daga kano zuwa kaduna.
tsoffin masu daukan nauyin, bankin shiga da fita ta kasar sin, ta janye daukan nauyin, ta baiwa bankin ci gaba ta sin kofar daukan nauyin.