Labaran Yau

An kona Gidaje A Kauyukan Jihar Filato

An kona Gidaje A Kauyukan Jihar Filato

An samu rahoton gidaje dayawa da aka kona bayan Yan banga wanda ke da Suna Operation Rainbow da ake zargi sun shiga kauyukan fulani dake karamar hukumar Mangu a jihar Filato.

Makiyayan sunce barasu iya kiyasce yawan mutanen da aka kashe ba, amma mutane dayawa sun mutu.

Makiyayan sun bayyana cewa yan bangan sun shigo karfe biyar na safe yayinda suka ta ruwa alburusai a kauyen, suka bi gidanjensu Suna saka wuta da bindigar APC armored personnel carrier, masu kona gidajen suka biyo a baya.

Shugaban wannan yan banga ta Operation Rainbow Sitdang Mungak, ya karyata wannan zargin cewa yayi rahoton ba daidai bane.

“Na nemi jami’un mu na Operation Rainbow Kuma Suna yan bangan Operation Rainbow basu kai wani farmaki ba. In akwai wani rahoton da bai da asali to ba daga wajen mu bane. Babu wasu bindigogin mu da yake aiki” Cewar sa.

Shugaban Miyetti Allah na jiha (MACBAN), Nuru Abdullahi, ya tabbatar da Farmakin da aka kai, yana Kuma kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shigo ciki kamin abin yafi karfin gyarawa.

“Mun yarda da cewa gwamnatin jiha bara ta iya magance wannan matsalar ba, Operation Rainbow ta jagoranci yan Ta’adda su kona gidajen mu, hakan ya nuna Suna shirye dan su koremu a Jihar Filato.

“Kamin wannan, an kona gidajen mambobin mu a Sarpal, Kombun, Rinago, Dtmirle, Kangang, Aloghom, Fongon, Bongangida, Luggere, Gaude, Jwaksham, Borwa, Luggadimesa, Tidiw da sauransu. Muna kiran Shugaban kasa Bola Tinubu ya kawo mana saukin wannan lamari” ya ce.

Isa Ibrahim Jamo daya daga cikin wanda farmakin ta shafa, ya ga abinda ya faru, yayi zargin jami’an tsaro sun kona gidaje a Changal, Kombili, lamor, washina, Gayam, anguwan Baraya, Vivim da yankin Jannaret.

“Dukiyar mu harda kayan sawan mu, katifu, taki da kayan abinci Duk an kona. Mata da yara da yawa sun gudu Gindiri da kasuwan Ali dan gudun abubuwan da zasu iya faruwa” Jamo ya ce.

Bayan kokari da akayi wajen yin magana da  Mai magana da yawun yan sanda na jihar, DSP Alfred Alabo, da na 3 division na sojin kasa na Barikin soji Rukuba, Lt Col Ishaku Sabastine Takwa basu dauki wayan da akayi musu ba dan samun bayani daga manema labarai.

Daily trust ta bada rahoton cewa ana ta samun rikici a kauyukan karamar hukumar mangu a watannin da suka gabata, fiye da mutum dari aka kashe harda mata da yara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button