Kunun aya yana daga cikin abun sha wanda yake da matukar dadi da amfani a jikin dan Adam. Domin kuwa Ana Hadawa ne da yayan itatuwa da madara. Yanada kyau musamman wa ma’aurata. Kina iya bawa Mai gida in ya dawo aiki Kuma Ki sauki baki dashi domin abun sha ne Mai kayatarwa.
Biyomu kadan dan ganin yadda Zamu hada kunun aya mai Dadi.
Kayan Hadi
i. Aya Kofi Hudu
ii. Dabino na Naira dari
iii. Kwakwa na naira Dari
iv. Suga ko zuma kofi daya
v. Madara kofi daya
vi. Flavor kadan inda hali
vii. Ruwa litre Biyu
Yadda Ake Hadawa
Da farko zaki wanke dabino, aya da kwakwanki Sannan Ki jika a ruwa na misalin minti talatin in bushashshiyar aya da dabino kike dashi.
Idan Kuma ba busassasu bane to babu ruwanki da jika wa Sai dai Ki wanke.
Sai ki zuba su cikin blender Ki markada, in yayi laushi sosai, Sai ki tace ki zubar da tsakuwar.
Domin tsakuwar zai iya hana jin dadin sha.
Bayan nan Sai a kara ruwa ya cika quantity na liter biyu.
Sannan Ki zuba madara, suga ko zuma Duk wanda aka fi so ko Ake da halin samu.
A gauraya a hankali Sannan a saka flavor kadan.
Sai a saka a cikin fridge dan yayi sanyi.
Kuma dan kar ya baci.
A zuba a kofi a sha dadi lafiya.
A kan iya sha da abinci ko cincin da sauransu.
Daga Nan Angama Hada Kunun Aya
Ga Yanda Ake Hada Wasu Girke Girken Daga Bisani ⇓