Shugaba Tinubu Ya Mika Sunayen Ministocin Sa Majalisa Don A Tantance Su
A yau ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai aika da jerin sunayen ministocinsa ga majalisar dattawa domin tantancewa, kamar yadda rahotanni suka iso mu a daren jiya talata.
Majiyoyin fadar shugaban kasa da na majalisar dattawa sun shaida mana cewa an shirya jerin sunayen ne domin mikawa zauren majalisar.
Wata majiya a fadar ta Villa ta ce: “An shirya jerin sunayen kuma shugaban kasar ya sanar da majalisar dattawa shirin sa na mika jerin sunayen a ranar Laraba. Ana sa ran shugaban majalisar dattawan zai karanta ta nan take idan ya samu.
“An kammala binciken tsaro da ya kamata, don haka shugaban kasa ya yanke shawarar aikewa majalisa. Ko yau ko gobe, takardar zata kai ga majalisar dattawa.”
Wani fitaccen dan majalisar ya ce majalisar dattawan na sa ran tantancewar a yau ko kuma gobe.
“An gaya mana cewa jerin za su zo mana ko dai yau ko gobe. Muna jira kuma muna shirye don aiki kan sunayen. Za mu kammala atisayen kafin mu tafi hutun shekara wanda zai dauki kimanin watanni biyu,” inji shi.
A ranar 17 ga watan Maris ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kudirin gyaran kundin tsarin mulkin kasar wanda ya umarci shugaban kasa da gwamnoni su mika sunayen mutanen da aka zaba a matsayin ministoci ko kwamishinoni cikin kwanaki 60 da rantsar da majalisar dattawa ko na jiha. .
An rantsar da Shugaba Tinubu ne a ranar 29 ga watan Mayu. Ya zuwa yanzu, ya shafe kwanaki 51 a matsayin shugaban Tarayyar Najeriya. A bisa doka, Tinubu yana da har zuwa ranar 27 ga Yuli ya gabatar da jerin sunayen.