Labaran Yau

Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutu Wa Kasa Dan Zagoyar Ranan Demokardiya

Gwamnatin Najeriya ta bada hutu wa kasa dan zagoyar ranan Demokardiya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar litinin 12 ga watan yuni, ranan hutu wa kasa dan murnan zagayowar ranan demokradiyya.

Jawabin ya fito daga bakin famanet Sakataren ministirin cikin gida na kasa, Dakta Oluwatoyin Akinlade, ranan Alhamis a Abuja.

Akinlade, wanda ta bayyana hutun a madadin Gwamnatin Tarayya, Ta taya yan Najeriya murna dan wannan rana.

Ta ce tafiyar demokradiyya a kasar ta samu koma baya da cigaba a wajaje dayawa, Amma Najeriya da yan Najeriya sun jajirce wajen tsayawa kan mulkin demokradiyya.

A ranan murnan zagayowar, yan Najeriya da abokan Najeriya Ana gayyata wajen murnan cigaban da aka samu da Kuma wanda za a samu a gaba na demokradiyya a kasar.” Ta ce.

Akinlade Tana taya murna wa Najeriya dan zagayowar ranan demokradiyya.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button