Labaran Yau

Gwamnatin Kano Yace Ba Ja Da Baya Wajen Rusa Gine Ginen Da Akayi Bisa Rashin Ka’ida

Gwamnatin Kano Yace ba ja da baya wajen rusa gine ginen da akayi bisa rashin ka’ida

Mai mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Gwarzo, yace babu ja da baya kan rushe gine ginen da akayi ba bisa tsarin gwamnati ba a garin Kano.

Gwarzo ya bayyana hakan a zaman su da mambobin kungiyar cigaba, a karamar hukumar taurani gidan gwamnati a daren Alhamis.

Ya bayyana muhimmancin bin doka dan daidaituwar doka da cigaban Birni da Kuma jaddada amfanin cigaban birni.

Mista Gwarzo ya nuna rashin kyau na gine ginen da akayi a rashin tsari da ka’ida kan kwalbati hanyan ruwa, hanyoyi da lafiyar mutane.

Mataimakin gwamna ya nuna illolin Sai da siyar da filin gwamnati da gwamnatin da gabata tayi, babu duba illar da zatayi kan Al’umma dan cimma burin su.

Ya bayyana rabawa da siyar da filayen wanda suka hada da na massalin idi da dadadden masallaci waje Mai tarihi Na karamar hukumar Fagge, yace filaye ne masu dunbun tarihi da muhimmanci wa Al’ada da Addini.

Gwarzo ya nuna bacin ransa kan siyar da filayen makabarta dan yin shaguna.

A cewar sa gidan Alhazai (hajj camp) an Rabata an sayar, duk da muhimmancin sa wajen lamuran Mahajja ta.

Gwamma Abba Yusuf ya dauki matakin kara gina gidan Alhazai da saka Duk abinda ake bukata a wajen.

A jawabin Nura dan’jani, ciyaman din kungiyar cigaba na karamar hukumar Tarauni, ya bada goyon bayan sa wajen rushe gine ginen aka yi ta hanyar da bai dace ba.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button