Labaran YauNEWSTrending Updates

IGP Ya Sanar Da Samun Labarin Muyagu Daga Ketare Dake Niyar Canja Manufan Zanga Zangar 1 Ga Wata

Babban Sufeta na 'yan sanda ya sanar da samun bayani akan sa hannun muyagun sojojin ketare a zanga zangar lumana da za a fara 1 ga watan augusta

A yaune jumu’a 26 ga watan yuli sufetan ‘yan sanda na kasa wato IGP Kayode Egbetokun ya sanar da samun labarin da sukayi na wasu mugayen na musamman daga ketare dake niyyar tada hankali a gun zanga zangar lumana.

Kamar yanda jaridar yanan gizo na Legit ta rawaito daga jaridar Vanguard, sunce sufetan ya bada shawarin rashin amfanin tirjiya da matasa ke yi kan zancen janye zanga zangar.

Yace lallai makiya kasa na nan na shirya mummunan manufa dan cinma burinsu a kan kasan Najeriya ne. Ya kara da cewa muyagun anyi hayansu ne dan yin sama da fadi da manufan zanga zanga ta lumana ta ‘yan kasa ke shirin yi.

Sannan kuma idan baza a manta ba zanga zangar Endsars ya koya wa mutane dayawa hankali gurin gane tashin hankali bayi da amfani wurin neman ci gaba.

Bayani daga bakin sufeto Kayode yayi da kansa amma a harcen turanci, yace; “Muna lura da wadanda suka yi magana kan duk wani nau’in zanga-zanga a wannan mawuyacin lokaci, saboda tsoron makiya kasarmu na iya yin magudin zabe.

“Mun tabbatar da cewa tsoronsu na gaskiya ne, saboda muna da sahihan bayanan sirri game da shigar sojojin haya na kasashen waje a cikin wannan zanga-zangar da aka shirya.”

Daga Karshe IGP yayi kira ga duk wanda yake da hanu akan jagorantar wannan zanga zanga da ya fito ya bada bayanan sa wa ‘yan sanda dan sani inda zasu tuhuma in abu ya kwace.

Sufeton yayi alwashin babu wanda zai iya fitowa ya karbi wannan jagorancin dan babu gaskiya a ciki, sai dai suta azizita wa a yanan gizo da shafin yada zumunta.

Jan Kunnen Barr. Daniel bayan Bayanin IGP Kayode Egbetokun

Rahoto Yazo da cewa Barr. Daniel Bwala, tsohon mai magana da yawun yakin neman zaben shugaban kasa ga Atiku Abubakar, ya ce zanga-zangar da ake yi a fadin kasar ba lallai ba ne a halin yanzu.

Bwala ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa ta Aso dake Abuja.

Masanin shari’ar ya ce dole ne ‘yan jam’iyyar adawa su ga bayan siyasa su hada kai da shugaba Tinubu a yunkurinsa na kawo sauyi ga tattalin arzikin Najeriya.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button