Kungiyar Manchester United a kakar bana
Bayan daukar Mason mount da Andre onana da kungiyar tayi, Manchester United ta kara shiga kasuwar sayan yan wasa. Wannan shine yadda ta kaya.
Batu Akan Rasmus Hõjlund
Manchester United na Shirin Kai tayi ga Atalanta cikin satin da muke ciki, Atalanta na ganin united zata Kai tayin ne ranar alhamis.
Atalanta ta sakawa dan wasan farashin kudi har euro million €65/70m, sai dai Ana ganin united bazata biya wannan kudin ba.
€50/55m shine adadin da ake tunanin united zata Kai idan har Atalanta Bata karba ba to united zata iya biyan €60
United ta kullah yarjejeniya da Hõjlund ya amince zaizo Manchester United domin itace kungiyar da yake so tun yana karami
Yadda ta kaya da Ambrabat
United na son Karin Dan wasan tsakiya, Wanda ake tunanin amrabat shine zabinsu saidai shima Dan wasan ya amince zaizo
A halin yanzu babu wata yarjejeniya tsakanin united da Florentina, sai dai United ta tabbatar da Neman da take yiwa Dan wasan
United na son kammala daukan Hõjlund kafin takai tayi Kan amrabat Kuma tanason sayar da Fred.
A wani cigaban kuma babu wata magana tsakanin united da wakilan Kane Tottenham Hõjlund shine united ke Burin dauka nanda wani lokaci.