Labaran Yau

Gwamnan Bauchi Ya Mikawa Majalisa Sunayen Sababbin Kwamishinoni

Gwamnan Bauchi Ya Mikawa Majalisa Sunayen Sababbin Kwamishinoni

Gwamnan jihar Bauchi Sen Bala Mohammed Abdulkadir ya aike da sakon zartarwa ga majalisar dokokin jihar inda ya bukaci ta tantance tare da tabbatar da sunayen wadanda ya nada a matsayin kwamishinoni da mambobin majalisar zartarwa ta jihar ta Bauchi.

Majalisar ta bayyana hakan ne yayin zaman majalisar da aka gudanar a ranar Litinin, wanda shugaban majalisar, Rt. Hon. Abubakar Y Sulaiman.

Shugaban Majalisar ya sanar da cewa Majalisar ta samu sako daga Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, inda ya bukaci ta tantance tare da tabbatar da wadanda aka zaba domin nada su a matsayin kwamishinoni da ‘yan majalisar zartarwa ta Jiha kamar yadda kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 ya tanada.

Yayin da yake gabatar da sakon Gwamnan a yayin zaman, shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Saleh Hodi Jibir, ya karanta sunayen wadanda aka nada.

Ga sunyen kamar haka:

Karamar hukumar Alkaleri: Maiwada Bello (Geo Barrister) da Ibrahim Gambo;
Bauchi: Mahmoud Babamaji Abubakar da kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar, Hon. Danlami Ahmed Kawule.
Bogoro: Tsammani Lydia Haruna.
Dambam: Ahmed Sarki Jalam.
Darazo: Yakubu Ibrahim Hamza.
Sauran wadanda aka zaba sun hada da:
Dass: Usman Santuraki.
Ganjuwa: Abdul Hassan.
Gamawa: Muhammad Salees.
Giade: Dr. Yakubu Adamu.
Jama’are: Usman Abdulkadir Moddibo.
Itas/Gadau: Hajara Jibrin Gidado.
Sauran sune
Katagum: Darakta Janar na Majalisar Kamfen din Gwamnonin PDP, Hon. Farouk Mustapha.
Kirfi: Hajara Yakubu Wanka.
Misau: Aminu Hammayo.
Ningi: Hassan El-Yakub SAN.
Shira: Muhammad Hamisu Shira.
Sauran wadanda aka nada sune
Tafawa Balewa: Silas Madugu, da Abubakar Abdulhamid Bununu.
Toro: Jamila Muhammad Dahiru da Dokta Adamu Umar Sambo.
Warji: Abdulrazak Nuhu Zaki.
Zaki: Amina Muhammad Katagum.
Hon. Barr. Habibu Umar mai wakiltar mazabar Kirfi ya ba da shawarar cewa majalisar ta tantance wadanda aka zaba a ranakun 2, 3, da 4 ga watan Agusta, 2023, kuma Hon. Lawan Dauda mai wakiltar mazabar Sade.
Bayan da shugaban majalisar ya gabatar da kudirin a kada kuri’a kuma ‘yan majalisar suka kada kuri’ar amincewa, majalisar ta yanke shawarar tantance wadanda aka nada a ranakun 2, 3 da 4 ga watan Agusta 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button