Kalli Bidiyon Ummi Rahab Tare Da Babanta Suna More Lokaci A Saudiyya
Alhamdulillah! Bayan tsawon cecekuce da jammaa sukayi abaya a kafafen sada zumunta akan masaniyar asalin mahaifin jarumar masana’antar Kannywood wanda akafi sani da Ummi Rahab, cikin ikon Allah sai ga jarumar ta hadu da asalin mahaifinta na jini a qasar Saudiyya.
A Baya Kadan Idan Mabiyan Labaranyau Baku Manta Ba Ita Tauraruwar Jarumar Kwanaki Ta Hadu Da Mahaifiyarta A Kasar Saudiyyar Wanda Har Suka Fashe Da Kuka Bayan Sun Dade Basu Hadu Ba, Daga Baya Ne Kuma Sai Gashi Tasamu Daman Ganawa Da Mahaifinta.
A Makwannin Baya Ne Dai Aka Dinga Yiwa Jaruma Ummi Rahab Din Gori, Kan Wasu Sun Fara Kokwanton Akan Asalinta Cewa Anya Tana Ma Da Iyaye Kuwa. Zuwa Yanzun Dai Jarumar Ta Bayyanawa Duniya Cewa Ita ‘Yar Sunnah Ce. Kuma Iyayenta Sunanan A Raye.
Ummi Rahab Din Tana Dab Da Amarcewa Tare Da Shahararren Mawaki Lilin Baba, Inda Akesa Ran Zasuyi Aurene Kafin Karshen Wannan Shekarar Da Muke Ciki.
Kalli Bidiyon Ummi Rahab Da Babanta