Labaran Yau

Daurawa Ya Dawo Matsayin Sa Na Shugabancin Hukumar Hisbah Na….

Daurawa Ya Dawo Matsayin Sa Na shugabancin Hukumar Hisbah Na Kano

Shahararren Malamin Addini Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda aka kara zaba a matsayin shugaban Hukumar Hisbah ta Kano, Gwamna Abba Yusuf Kabir ya kara zaben sa ne bayan canji da ya gani a Hukumar.

Daurawa ya bayyana zaben shi a shafin sa ta Facebook a bidiyo da yayi ya wallafa ranan litinin.

Zai jagoranci Hukumar Hisbah na uku kenan, bayan yayi sau biyu karkashin gwamnatin tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnati Abdullahi Umar Ganduje ta farko.

DOWNLOAD MP3

Sheikh Daurawa
Sheikh Daurawa

A shekarar 2018, ya ajiye aikin saboda rikicin da ke tsakanin tsoffin gwamnonin biyu kwankwaso da Ganduje.

Malamin ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook, yana karban takardan zaben sa na matsayin da ya samu daga hannun sakataren gwamnatin jiha, Abdullahi Baffa Bichi.

Malamin wanda ya zama shugaban Hisbah ya taka rawa wajen kawo Gwamnatin jam’iyyar NNPP, an ga taimako da yayi sosai a zaben da ta gabata na shekarar 2023.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button