Labaran Yau

Fusatattun Matasa Sun Kashe Daya, Sun Kona Gida 64 Da Babura Uku..

Fusatattun matasa sun kashe daya, sun Kona gida 64 da babura uku a Bauchi

Hukumar yan sanda a Bauchi sun bayyana cewa fusatattun matasa sun kona gidaje 64, babura 3, aka rasa ran mutum daya. Da tarwatsa dukiya kimanin miliyiyo a karamar hukumar Bogoro ta jihar.

Bayanin yafito daga bakin Ahmed Wakili wanda keh magana da yawun yan sandan koman din zuwa manema labarai ran lahadi a garin Bauchi.

Yace hakan ya biyo bayan bikin sarautar sarkin sang da akayi wanda bai ma dayawa dadi ba ya fusata matasan garin ya kai da tashin hankali.

DOWNLOAD HERE

Ran Asabar ran 15 ga watan Aprailu a shekarar 2023, da misalin karfe 7 na Yamma ofishin yan sandan suka samu rahoton tarzoman dake afkuwa a karamar hukumar Bogoro, a cewar wakil .

Ya kara da cewa mutum daya Apollos Danlami meh shekaru 70, ya rasa ransa a hanun matasan, Naemiya Bature meh shekaru 66 da wasu mutanen sun samu rauni a dalillin tashin hankalin.

Meh magana da yawun yan sandan ya bayyana cewa yan sandan sunyi kokari wajen zuwa bayan kira da aka musu wanda ya kawo karshen tarzoma.

DOWNLOAD MP3 HERE

Kuma an karo jami’an tsaro dan Samar da zaman lafiya a garin Bogoro.

Yace kwamishinan yan sandan jiha Aminu Alhassan ya baiwa DPO a garin Bogoro dama dan yin bincike a boye dan kawo sulhu wa matsalar.

Ana yin kokari dan samo hujjar da zaisa a kama Duk wanda suka haddasa matsalar.

Daily Nigeria ta rawaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button