Labaran Yau

Betara Na Zargin Gbajabiamila Da Bawa Wani Goyon Baya Kan….

Betara na Zargin Gbajabiamila da bawa Wani goyon baya kan shugabancin tarayya

Dan Majalisan tarayya wanda ke wakilta daga jihar borno Aliyu Betara, ya bayyana kudirin sa na zama shugaban Majalisan tarayya na Goma, kamin 5 ga watan yuni.

Betara ya zargi Shugaban Majalisan tarayya da bada goyon baya wa wanda baiyi suna ba ya gaje shi.

Shi Betara ya kasance chairman na Appropriation, ya bayyana kudirinsa na neman shugabancin Majalisan a Abuuja inda yayi korafin.

DOWNLOAD ZIP/MP3

A taron da akayi a transcorp hotel, Betara yana tare da yan takarun kamar su Ahmed Wase mataimakin Shugaban Majalisan, Alhassan Doguwa, Sani Jaji da Tunji Olawuyi.

Wasu daga cikin wanda suka halacci taron akwai zababben gwamna Umar Bago, wanda har a yanzu dan Majalisan tarayya ne Kuma magoyin bayan betara ne.

Hukumar labarai ta kasa ta bada rahoton cewa wasu sabbin yan Majalisun daga wasu jam’iyu duk halarta.

Jam’iyyar APC ta zauna ta zabi yankin da zasu yi Shugaban cin Majalisan dattawa dana tarayya, inda aka zabi Shugaban yazo daga Arewa maso Yamma, mataimakin yazo daga kudu maso gabas.

A inda suka bada umurni Abbas Tajudeen ya zama shugaban Majalisan kuma Benjamin kalu yazama mataimakin Shugaban Majalisan.

Bayan rahoton ya fito, betara ya bayyana takarar zama shugaban Majalisan tarayya.

Yace yaji mamakin zaban Abbas da Gbajabiamila yayi bayan dayawa daga cikin su sun nuna Suna son takarar.

“In yau mataimakin Shugaban Majalisan tarayya yana takara, jagoran Majalisan tarayya yana takara da shi chairman na appropriation yana takara, wa yafi kusanci da Shugaban” a cewar sa.

Jami’an tsaro sun dau lokaci wajen binciken yan Majalisu da zasu iya kawo tarzoma a wajen taron.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button