Labaran Yau

Banyi Nadaman Bayyana Sakamakon Zaben Adamawa Ba Cewar Ari

Banyi Nadaman Bayyana Sakamakon Zaben Adamawa ba cewar Ari

Saukekken kwamishinan zabe na Jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, Yace baiyi nadaman bayyana Binani a matsayin zababben gwamnan jihar Adamawa ba a zaben da ta gabata.

Ran 16 ga watan Aprailu, yayi amfani da karfin da ba nashi ba wajen bayyana sakamakon zabe wanda ba hurumin shi bane.

A lokacin da ya bayyana, sakamakon kananan hukumomi goma ne kawai a kasa cikin 20 wanda aka hada aka kirga.

Cikin kankanin lokaci hukumar Zabe ta kasa ta bayyana wannan sakamakon ba yi da tasiri kuma bashi bane sakamakon zaben. Kuma ya kai da sauke shi a matsayin sa.

A hirar da yayi da BBC ya bayyana cewa shi bai karbi cin hanci ba dan ya bayyana sakamakon zabe ba.

“ Ban ce wa gwamna ko Binani su bani cin hanci ba, dan hakan baya cikin tsarin addini na. Zargi da akeyi kan cewa an bani biliyan biyu karya ce, jitajita ce”

“A Ina Zan kai biliyan biyu? Nagani a shafin sada zumunta Wai an bani biliyan biyu”. A cewar sa.

An tambayeshi yayi nadama? Yace baiyi ba. Kuma ya kara jaddada cewa Binani taci zabe.

“Duk abinda zakayi cikin doka, to barakayi na dama ba. Aisha binani taci zabe kuma komai yana bayyane a takardan”.

Yace shi bai gudu buya ba, kuma zai je in yan sanda sun gayyace shi.

“Na rubuta takarda wa Hukumar zabe ta kasa, sun ce barasu karba ba amma nasan sun karba. Kuma idan yan sanda suka gayyaceni dole zanje”

“Ban gudu zuwa ko Ina ba, Kuma zanje wajen yan sanda in sun kirani” cewar sa

Yau Talata yan sanda sun ka kama Barista Hudu Ari

Da safe ya bayyana cewa bai yi na daman bayyana sakamakon zaben na cewar Sanata Aisha Binani ne ta lashe zaben Gwamna da ta gabata.

Insifeto janar din yan sanda ya bada umurnin a kama Duk mai ruwa da tsaki wajen bayyana sakamakon zaben da akayi ba akan doka ba ta jawo tarzoma.

A halin da ake ciki, dan sanda Muyiwa Adejobi ya tabbatar cewa Ari Hudu yana garkame a hanun su.

Wa inda suka taimaka acikin jami’un Suna amsa tambayoyi su ma a hannun yan sandan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button