Labaran Yau

Majalisan Tarayya Zata Bincike Hukumomi, Jami’o’i Da Sauransu Kan Siyar Da Aiki

Majalisan Tarayya Zata Bincike Hukumomi, Jami’o’i Da Sauransu Kan Siyar Da Aiki

Majalisan tarayya ta amince da kirkiran kwamiti dan binciken Ministirin Tarayya, departments da hukumomi da jami’o’i  kan zargin rashin ka’ida ta daukar Ma’aikata, da rashin bin dokar biyan Albashi na IPPIS.

Hakan ya biyo baya kan korafin Oluwola Oke dan PDP daga jihar Osun a zaman majalisa na ranan laraba.

Majalisan ta ce Gwamnatin Tarayya tayi kokarin gyara akan rashin bin doka da kuma magance matsalar Ma’aikatan da babu su (ghost workers).

Sun kara da jawabin cewa hakan yasa aka kawo tsarin IPPIS na biyan Ma’aikata dan gano Ma’aikatan boye ghost workers.

A korafin Oke, ya bayyana cewa daukan aikin gwamnati ya baci da rashin bin doka da rashawa wanda ta ke a bayyane.

Yace, “Hukumomin sun daina bayyana daukan aiki Duk lokacin da aka samu wuraren da yakamata a dau Ma’aikata, Kuma a lokutan da aka bayyana Ana neman aiki, wannan wuraren an bada su wa wasu daidaiku dan su kawo nasu mutanen, aikin yanzu siyarwa akeyi wa wanda yake da kudade.

“Hukumomi Suna siyar da aikin ba tare da duba cancanta ba wajen aiwatar da aiki mafi inganci.

“Kuma sun kawo hanya wanda ake amfani da su wajen kare BVN, wanda hakan yana sa Gwamnatin Tarayya kashe biliyoyin kudade a wata dan biyan albashin wanda basu aiki da Kuma biyan Ma’aikata a bisa rashin tsari da doka a kawoni matsayi na aikin gwamnati.

“Hakan ya kawo rashin tsari wanda ya taimaka wajen kawo rashin ingancin aiki wa kasa gabadaya.

“Tun daga tarihi, a shekarar 1960 zuwa 1990, Najeriya tana alfahari da kawo Ma’aikata wanda suka dace da aikin da Kuma yin aiki bisa kwarewa.

“Lamarin ya jima da rugujewa saboda hanyar da ake bi na daukan aiki wanda ke aukuwa ta hanyar rashawa da rashin bin ka’idar daukan aikin”.

Majalisan ta kirkiro kwamiti dan bincike akan Hukumomi, jami’o’i da sauransu Kuma su dawo da rahoto dan daukan mataki nan da sati hudu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button