Labaran Yau

Hukumar Rashawa Ta Jihar Kano Ta Wanke Daily Nigerian Da Bayyana Bodiyon Dalar Ganduje Gaskiya

Hukumar Rashawa Ta Jihar Kano Ta Wanke Daily Nigerian Da Bayyana Bodiyon Dalar Ganduje Gaskiya

Shugaban Hukumar yaki da rashawa ta jihar kano Muhuyi Rimingado ranan laraba yace sunyi forensic bincike kan bidiyon da ya nuna cewa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje yana karbar Dala daga hannun dan kwangila.

A shekarar 2018, Daily Nigerian ta wallafa bidiyon dalar, wanda shi gwamna ya nuna cewa ai hadawa akayi.

Rimingado ya bayyana abinda suka samo a bincike na forensic akan bidiyon a wajen wani taro da akayi kan rashawa Na wuni daya, cewa sun samu tabbacin cewar bidiyon Gaskiya ne.

DOWNLOAD MP3

Tun bayan fitowar bidiyon, mutane sun  takura mana akan muyi bincike dan su tabbatar da gaskiyar lamarin akan tsohon gwamna.

 

Ya kara da cewa sun fara binciken a shekarar 2018 amma basuyi nisa ba saboda Ganduje yana da rigar kariya a Wannan lokacin.

DOWNLOAD ZIP

Ran 14 ga watan Yuni, Ganduje yace wa kotun kasa na Kano cewa su hana EFCC kan binciken shi akan bidiyon da ya fito wanda ta nuna shi yana karban dala a wajen dan kwangila.

A karar da aka kai kotun kasa, tsohon atoni janar na jiha M.A Lawan ya nemi kotu ta hana Hukumar Rashawa daga bincikar Ganduje har Sai an gama gudanar da kara da ke tsakanin Ganduje da Mawallafin daily Nigerian Jaafar Jaafar ta kammalu.

Hukumar EFCC ita ce kadai Mai Kare kanta a karar.

Ganduje ya nemi Kotu ta bayyana gayyata da binciken ciyaman na Subeb na jihar kano a matsayin rashin tsari na doka, da tsohon akanta janar na jihar wanda Suna da alaqa da bidiyon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button