Hukumar zabe ta Kasa INEC ta bayyana ranar karasa zaben Kebbi da Adamawa
Hukumar zabe ta bayyana Cewar zata gudanar da zaben gwamnoni wanda suka rage da yan majalisun jaha dana tarayya ran sha biyar ga watan hudu a fadin kasa gaba daya.
Kammalallun zaben gwamnoni guda Ashirin da shida (26), sanatoci dari da hudu (104), yan majalisan tarayya dari uku da ashirin da tara (329), yan majalisan jaha dari tara da talatin da biyar (935) INEC ta bayyana cin zaben su.
Inda zaben ya shafa wanda za gudanar a watan hudu ya kunshi na gwamnoni na jihar kebbi da Adamawa, Sanatoci guda biyar, yan majalisun tarayya guda talatin da daya da Kuma yan majalisun jiha guda hamsin da takwas a fadin najeriya.
Daga bakin jami’i mai magana da yawun INEC, Festus Okoye ya bayyana cewa ba duka mazabun za ayi zabe ba a wanda ya shafi na yan majalisu ba. Za ayi ne a zababbun polling units wanda hargitsi da badakala ya shafa har yakai da sakewa.
Ya kara da cewa zasu bayyana inda za ayi zaben da Kuma wainda zasu yi zaben da yawansu a shafin website din Inec ran Ashirin da tara ga watan maris.
Kuma Ana gargadi wa dukan jam’Iyar da zasu kasance a wannan zaben da su kasance masu nutsuwa da rashin tashin hankali wanda zai kawo cikas wajen sakamon zaben na za a aiwatar ran sha biyar ga watan hudu.