Labaran Yau

Mutane 6 Sun Rasa Rayukan Su Sakamakon Wani Harin Wuka Da Aka Kai A Makarantar Kananan Yara A…

Mutane 6 Sun Rasa Rayukan Su Sakamakon Wani Harin Wuka Da Aka Kai A Makarantar Kananan Yara A Kasar Chine

Mutane 6 ne ake fargabar sun mutu yayin da daya ya jikkata a wani harin wuka da aka kai da sanyin safiyar Litinin a wajen wata makarantar renon yara a kudancin kasar China.

Kafar labarai ta CNN ce ta ruwaito lamarin wanda ya faru da misalin karfe 7:40 na safe a garin Hengshan da ke cikin Lianjiang na lardin Guangdong a kasar ta China.

Sanarwar da ‘yan sanda da kafofin yada labaran China suka fitar sun ce harin da “rauni ne da gangan” inda suka kara da cewa maharin ya yi amfani da wuka kuma har yanzu ‘yan sanda na tabbatar da sunayen wadanda abin ya shafa.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, wadanda suka jikkata sun hada da malami daya, iyaye biyu da kuma yara uku, kamar yadda shaidu suka tabbatar.

‘Yan sanda sun kama wanda ake zargin, wani matashi dan shekara 25 mai suna Wu, jim kadan da misalin karfe 8 na safe. Yanzu haka dai ana gudanar da bincike kan lamarin, a cewar sanarwar.

Hotunan faifan bidiyo daga wurin da lamarin ya faru, wanda aka yada ta kan layi sannan kuma aka samu tare da rarrabawa daga kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya nuna harin da aka kai a wajen wata makarantar yara.

Bidiyon ya nuna yadda mazauna yankin ke wucewa ta wurin da aka kai harin, inda wata alama a waje ta rubuta

“Kindergarten,” da kuma sanya faifan ‘yan sanda.

Kasar Sin wato China ta fuskanci yawaitar hare-haren wuce gona da iri a cikin ‘yan shekarun nan, inda galibi ake kai wa yara hari; Wani harin wuka da aka kai a shekara ta 2020 a wata makarantar firamare ya raunata yara 37 a kudancin yankin Guangxi, yayin da a shekarar 2022 aka kashe uku a wata makarantar renon yara a gabashin lardin Jiangxi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button