Buhari Ya sallami Saratu Umar Shugaban NIPC
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya katse shugaban cin Saratu Umar a matsayin babban sakatare/ babban Jami’ar hukumar kula da cigaban saka hannun jari ta kasa nan da nan.
Femi Adesina, Meh magana da yawun shugaban kasa ya bayyana wannan cigaban ne ranan Alhamis da ta gabata a Abuja.
A umurnin da aka bawa ministan kasuwanci, kampanoni da hannun jari, Adeneyi Adebayo, shugaban kasa ya umurce shi da bawa rikon qwarya ga darekta mafi girma dan kula da hukumar.
Hukumar labarai ta kasa ta bayyana shugaba buhari ya sabonta mata shugaban cin na shekara biyar watan yuli 2022.
Daily Nigeria ta rawaito cewa an bata mukamin ne tun a shekarar 2014.