Gagdi ya bayyana kudirinsa na neman shugabancin Majalisan tarayya
Dan Majalisan tarayya daga jihar Plateau dan jam’iyyar APC Yusuf Gagdi. Ya bayyana burin zama Shugaban Majalisan tarayya na goma, da alkawarin biyan bukatu na mutane.
Gagdi, wanda yake neman Shugabanci karkashin “kasa daya, cigaba tare”, ya bayyana hakan a transcorp hotel din da ke Abuja ran Asabar.
Dan Majalisan wanda shine Shugaban kwamitin Navy yace a karkashin shi zai tabbatar da tsarin demokradiyya.
Ya kara da cewa Majalisan zata zama gida ne wanda kowani dan majalisa ke wakiltar wurinsu, bara’a dau majalisan da wasa ba.
Yayi alkawarin dawo da martaban Majalisan tarayya da ajandar aikinta ta tsantsa, Kuma ya kara alkawarin kawo dokar Majalisa Mai yanci.
A bayanin yace zasu yi aiki tukuru na bawa Majalisan karfi wajen saka ido akan lamuran gudanar da gwamnati da kuma gyara mai inganci.
Mohammed kazaure dan Majalisa mai wakilta daga jihar jigawa masoyin Gagdi, Yace Yusuf ya kasance gwani cikin gwanaye, yayi magana a wurin kan a mara wa Gagdi baya.
Sanata Mai wakilta daga jihar Pilato Diket Plang, yace “Gagdi mutum ne Mai hazaka, saboda shi mutan pilato sunci moriyar demokradiyya wanda ake gani zahiri a fili”.
Plang ya bayyana cewa gagdi ya damu da cigaban Al’ummq ne kuma bai da kabilanci na yare ko addini.
Hukumar labarai ta kasa ta bayyana cewa sabbin yan majilisu da wanda Kuma suka dawo, Yan jam’iyyar APC da wanda ba nasu ba sun taru wajen mara wa Gagdi baya.
Daily Nigeria ta rawaito