Labaran Yau

Dalibai 80,000 Ne Suka Rubuta Jamb Bayan Rasa Zaman Farko

Dalibai 80,000 ne suka rubuta Jamb bayan rasa zaman Farko

Sama da dalibai dubu 80 suka samu zaman rubuta jarabawan jamb wanda aka kara rubutawa a fadin kasar.

Fabian Benjamin, Mai magana da yawun Hukumar jarabawan,ya bayyana hakan bayan zagawa da yayi a wuraren da ake rubuta jarabawan a Abuja.

Benjamin yace a kalla dalibai dubu tamanin wanda basu samu zaman rubuta jarabawan ba saboda dalilai daban daban a lokacin da akayi, Sai aka kara saka musu ranan da zasuyi gaba daya kasan.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Wanda rashin rubuta jarabawan ya shafa harda wanda aka tantance, da wanda aka kasa yi musu tantance wa na yatsu da sauransu basu samu sunyi ba. Mafi yawa ba laifinsu bane.

Benjamin Yace sabbin hanyoyi da suka kawo ya hana badakala a wajen rubuta jarabawan, wanda hakan yasa an samu karancin badakala jarabawa.

Magana kan sakamakon jarabawan, Hukumar zata yi zama akai don kawo maslaha game Bayan an kammala komai na jarabawan da aka sake yi.

Ministan ilimi na kasa, Adamu Adamu, yana daga cikin wanda suka zaga wuraren jarabawan tare da rajistaran Hukumar jamb din Farfesa Ishaq Olodeye, sun bayyana gamsuwan su ga jarabawan da aka sake rubutawa na shekarar 2023.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button