Kungiyar Manchester United Na Shirin Nada Sabon Kaftin
A yau ne kaftin din Manchester United kuma Dan kasar ingila wato harry Maguire ya wallafa labarin a shafinsa na tuwita. Dan wasan yace “Bayan tattaunawa da kocin kungiyar wato Erik ten haag, ya sanar dani shirinsa na canja kaftin din da zai jagoranci kungiyar a kakar wasanni mai zuwa kuma ya fadamin dalilansa.
Dan wasan dan shekara 30 da haihuwa ya kara da cewa, ina matukar bakin cikin wannan hukunci amma zan cigaba da bada gudummawa dari bisa dari duk lokacin da na saka wannan riga mai dimbin tarihi. Tun lokacin da na karbi wannan matsayi shekara uku da rabi da suka wuce, wannan yana cikin abu mafi alfahari a rayuwa ta ta kwallon kafa.
Wato jagorantar wannan kungiya. Sannan ya kara da cewa yana mai godiya ga tsohon kocin kungiyar wato Ole daya bashi wannan shugabanci, sannan ya kara da cewa zai bawa duk wanda aka nada a matsayin sabon kaftin hadin kai domin kai wannan kungiya ga ci.
Dan wasan bayan na kasar ingila Wanda Manchester United suka siya akan fam miliyan tamanin ya fuskanci matsi sosai saboda gazawarsa a cikin fili, tun kafin kakar wasanni ta bana ta kare magoya bayan kungiyar sunyi ta kira ga mai horaswa Erik ten haag daya canja musu jagoranci.
Ana sa rai Dan wasan tsakiya na kungiyar kuma Dan kasar Portugal wato bruno Fernandes shine zai jagoranci wannan kungiya a kakar wasanni mai zuwa.