Tinubu ya zabi Bagudu da tsohon kwamishinan kudi ta jihar legas a kwamitin shirye-shiryen gudanar da bawa karagar mulki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Boss Mustapha ya jagoranci kwamitin shirye shirye da tsare-tsare wajen gudanar da bada karagar mulki ga sabon shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu, wanda za ayi ranan Ashirin da Tara ga watan mayun shekara ta dubu biyu da uku.
Shugaban kasa meh jiran Gado Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zabi gwamnan jihar kebbi Atiku bagudu da tsohon kwamishinan kudi na legas Wale Edun. Don gudanar da tsare-tsare wajen rantsar da sabon shugaban.
Boss Mustafa ya bayyana cewa kwamitin mutum 24 ne wanda a kalla Ana bugatan shugaba Meh jiran gado ya bada mutum biyu ciki Kuma ya bada.
Ya kara cewa ya kasa kwamitin gida uku domin shirye shiryen gudanar da bikin Mika taragar mulki cikin lumana ranar 29 ga watan mayu.
Tun bayan kammala zabe, kwamitin sun hadu don tattaunawa so hudu.
Kwamiti na farko cikin kwamitin sun fara tsare tsare na rantsarwa da Kuma pareti wanda yazama al’ada ne kowani lokacin rantsar da shugaba a Najeriya.
Shi Mista Mustafa shi keh jagoran wannan kwamiti. Da Kuma kwamitin goma sha kar Kashin wannan kwamitin wanda suka kunshi ciyarwa, sanarwa, sadarwa, rantsarwa da sauransu
Kwamiti na biyu Kuma ta kunshi shirya takardun mika taragar mulki wanda shugaban ma aikata na kasa gaba daya zai jagoran ta domin hado kan duka takardun gudanar wa na gwamnatin gaba daya da abinda suka aiwatar na dukkan al’amuran gwamnatin tarayya.
Gwamna me jiran gado a Kano Abba zai amshi Takardar sa na cin zabe.
A yau Laraba 29 ga watan Maris, Abba kabir Yusuf wanda aka fi Sani da Abba gida gida, ya shirya tsaff domin karban takardar shaidan cin zaben sa a matsayin gwamna a jihar Kano.
Abba ya kasance kwamishinan Ayyuka a gwamnatin Sanata Rabiu Musa kwankwaso a jihar Kano daga shekarar dubu biyu da sha daya zuwa dubu biyu da sha biyar.