Siffar Macen Da Zaku Aura Na Albani Zaria
Sharuda na farko akan macen da zaku aura yazama cewa tana ta Addini kuma ta zamto ta fito gida nagari, idan tana da addini, Amma gidansu mutanen banza ne ka kauce mata, tana da addini gidan su yan bidi’a ne ka kauce mata.
Tana da addini gidansu mushrikai ne ka kauce mata, tana da addini gidansu yan boko ne ka kauce mata, Yakamata ka lura da wannan.
Lallai sai ansamu tana da Addini gidansu na da addini. Amma in ya kasance tana da addini Amma iyayenta mushrikai ne suna tsafi, ko yan bidi’a ne, ko yan Al’ada ne, ko yan boko ne ko yan siyasa ne, rayuwa suka tusa a gaba addini bata damesu ba, kana ganin ita zaka zauna ba da iyayenta ba. To sai kayi nadama Saboda irin abubuwan da muka gani cikin rayuwa dan gane da auren irin wadannan mata daga irin wannan gidaje. Ha’inci ne idan malamai basu fito sun fada wa mutane gaskiya dangane da ire iren wannan matsaloli.
Galibin abinda ke rudan matasa shine yan mata masu hadda, masu sanya hijabi da niqabi amma wani gida ta fito? Ka taba ganin inda masara ta fito a cikin kashi ?
Masara tana fitowa a cikin kashi, a juya kashi a matsayin taki zata fitar da masara, siffar da annabi ya bayyana kenan kan macen da ta ke da kyau ta fito daga mugun gida.
Ga ta kakkyawa, Amma iyayenta da kankanin ta fa? Miyagu ne, kauce mata kawai. Saboda haka kowa ya nutsu ka duba da kyau. Ka duba sayyida Aisha Malama ce, mu’umina ce, musulma ce, daga cikin assbiqaat, tana da daga cikin yan gwagwarmaya.
Aisha RA cewa tayi tashi tayi taga uwata da ubana suna sallah, kuma tashi tayi taga mahaifin ana gwagwarmaya dashi dan ya Gina masallaci a kofar gidansa a makkah, gidan addini kenan. To waye mijinta Annabi SAW. Matasa ku nutsu ku duba kamin auro mace.