Girke GirkeLabaran Yau

Yadda Ake Gwaten Doya (Yam Porridge)

Yadda Ake Gwaten Doya (Yam Porridge)

Doya ana sarrafa shi hanya daban daban, Kuma Ana cin doya a wajaje dayawa, yau zamu kawo muku Yadda ake Gwaten doya cikin kankanin lokaci cikin sauki.

Kayan Hadi

DOWNLOAD ZIP/MP3

Doya Rabin doya in babba ne
Attaruhu na 50 naira
Tattasai na 100naira
Albasa biyu manya
Citta  na 50 naira
Tafarnuwa na 50naira
Nama na 500
Bushasshen kifi na 300naira
Ganye(alaiyahu na 50 naira ko ugu na 100naira ko ganyen albasa)

Yadda Ake Hadawa

Dafarko zaki fere doya ki yayyanka daidai yadda kikeso kisa a tukunya kisa gishiri kadan da sugar idan kinaso Shima na Kara mishi wani dadi.

Kamin nan sai ki wanke nama kisa citta da tafarnuwa,Albasa, Maggie kamar guda 7 da gishiri kadan idan yadau nuna bayan minti sha biyar sai ki wanke bushasshen kifi ki saka su dahu tare idan yayi sai ki juye akan doyan wanda yana cikin tukunya a kasa.

Sai ki daura a kan wuta.

Bayan Nan sai kisa markadadden attaruhu da tattasai da albasa daidai yanda kikeso manja da Maggie sai kisa ruwa kadan saboda komi ya riga ya dahu.

Yadda Ake Gwaten Doya (Yam Porridge)
Yadda Ake Gwaten Doya (Yam Porridge)

Bayan wasu minti sha biyar sai ki zuba ganye ko alaiyahu ko ugu ko ganyen albasa duk Wanda de kakeso bayan kin yanka kin wanke, idan ya nuna a sauke bayan minti goma.

Gwaten doya yayi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button