Labaran YauNEWS

Hon Kasimu Haruna Ya Siya Fom Din Takarar Majalisar Jiha

Hon Kasimu Haruna Ya Siya Fom Din Takarar Majalisar Jiha Mai Shirin Wakilcin Alummar Mazabar Zing, Jihar  Taraba

Hon Kasimu Haruna Na Jihar Taraba Yasamu Zarafin Zuwa ofishin Jamiyyar PRP Reshen jihar Taraba tare da Wakilcin wasu daga cikin magoya bayanshi don karban form din nuna sha’awar takara da form din takaran kujerar Majalisar Jiha Mai Shirin Wakilcin Alummar Mazabar Zing A Majalisar Jihar Taraba A Zabe mai zuwa na 2023.

Bayan karban form din ta hannun shuwagabannjn Jamiyyar na jihar Taraba  Hon Kasimu Haruna yayi Alwashin idan Allah ya bashi nasara zasu kau da irin salon mulkin da dan takaran baya yakeyi na rashin ko inkula da alumma.

Sakon Barka Da Sallah- Hon Kasimu Haruna

A jawabinshi yayi alkawarin kawo karshen rabuwar kai da ake samu tsakanin Yarrurrukan dasuke wannan yanki nasu na Zing tare da Fatan Alumma dasu fito don zaban chancanta.

Yayi Addu’an Allah yasa ayi zabe Lafiya tare da fatan Alkhairi ga Ilahirin Alummar Kasar Zing.

 

DOWNLOAD ZIP/MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button