Alummar Wani Gari Sun Ciro Tsoro Sun Afkawa Dan Bindiga
Kawo zuwa yanzu al’umma sun fara cire tsoro inda suka dauki matakin tunkarar ‘yan bindiga da duk karfinsu domin tsananin halin da aka shiga musamman a jihar Kaduna.
Inda wasu fusatattun mutanen gari sun cafke tare da lakada wa daya daga cikin ‘yan bindigan da ake zargi da sune suka kai hari a unguwar Bulus da Gimbiya a cikin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, wanda sakamakon hakan ya rasa ransa.
A wani sabon harin da ‘yan bindiga suka kaddamar a yankunan a daren jiya Alhamis ya janyo rasa rayukan mutanen yankin uku wanda hakan ya fusata jama’a matuka.
Rahotonnin da suka fito na nuni da cewa mazauna yankin sun tabbatar da cewa a ranar Alhamis din ‘yan bindigan sun shafe tsawon awanni suna cin karensu babu babbaka lamarin da ya janyo jama’a suka tashi tsaye domin kare kansu biyo baya yadda tura ta kaisu bango.
Daya daga cikin wadanda suka rasa ‘yan uwansu, Mista Ben Maigari ya ce ‘yan bindigar sun kashe wani yaron dan uwansa sannan suka sace mahaifinsa a yayin harin da suka kai Unguwar Bulus.
Mun jiyo karar harbin bindiga tun kafin dare ya raba don mutane da yawa ba su kwanta ba. Sai bayan komai ya lafa muka samu labarin sun kashe yaron dan uwana sannan sun yi awon gaba da mahaifinsa.
Ya kara da cewa, bayan nasa dan uwan da aka kashe, wasu mutum biyu na al’umman yankin su ma sun rasu sakamakon harin ‘yan bindiga, inda ya tabbatar da cewa jama’an garin su kuma sun yi kukan kura inda suka kashe daya daga cikin ‘yan bindigan.
An yi kokarin jin tab akin jami’in watsa labarai na ‘yan sandan jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige amma haka bata cimma ruwa ba.