Labaran Yau

Jihar Nasarawa Ta Samu Shugabannin Majalisan Jiha Biyu

Jihar Nasarawa ta samu shugabannin Majalisan jiha biyu

Akwai rudani a Majalisan jihar nasarawa, bayan hawan shugabanni biyu a kujerar.

Daily Nigeria ta bada rahoton cewa da Tsohon shugaban Majalisan Ibrahim Balarabe, da sabon shugaban Majalisan jiha Daniel Ogazi, wanda ya hau kujerar ta hanyar zaben da akayi ranan talata a wani wuri ba fadar Majalisan ba.

Rudanin ya fara ne, yayin da sabbin yan majalisa suka isa wajen rantsar dasu inda aka fada musu cewa an daga rantsar wa a fadar Majalisan jiha ta lafiya.

Mai rikon kilakin Majalisan Ibrahim Musa, yayi bayanin ran talata cewa daga rantsar wan yazo ne bayan rahoton tsaro da ya isan ma gwamna Abdullahi SULE.

Ogazi, wanda ya samu kuri’un wanda suka goya masa baya mutum 13, sun ki su bar fadar Majalisan yayin da Ogazi yaci zaben shugaban Majalisan jiha da kuri’u 14.

Bayan haka, a lokacin da aka samu labarin daga rantsar war. Balarabe wanda ya samu goyon bayan gwamna, ya tafi ministirin karamar hukuma da masarautun gargajiya sukayi nasu zaben.

Kuma shima yazama shugaban Majalisan jiha da kuri’u goma.

Messrs Balarabe da Ogazi duka yan jam’iyyar APC ne.

Ogazi ya zabi Muhammad Oyanki a matsayin mataimaki, Jacob kudu kuma mataimakin Balarabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button