Labaran YauNEWS

Sakon Sarkin Musulmi Ga Yen Kasuwa – Watan Ramadana

Sakon Sarkin Musulmi Ga Yen Kasuwa – Watan Ramadana

Mai alfarma Sarkin Musulmai, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ja hankulan yan kasuwa dake fadin kasar nan da su ji tsoron Allah kada su kara farashin kayayyakin masarufi a lokacin watan Ramadana, yana mai cewa babu wani ribar da za su samu bisa tsauwala wa masu azumi.

Da ya ke jawabi a wajen rufe gasar karatun Alkur’ani karo na 36 da ya gudana a jihar Bauchi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya jawo hankalin al’ummar musulmai da a kowani lokaci su rika amfani da koyarwar Alkur’ani domin neman tsira duniya da lahira.

A gefe daya, ya fadakar da al’ummar musulmai dangane da gabatowar watan Ramadana, yana mai cewa wata ne mai dumbin falala da albarka, sai ya jawo hankalin musulmai da su dukufa ibada sosai domin neman tsira duniya da lahira.

Da yake gargadi ga ‘yan kasuwan, Sultan ya ce watan Azumi, lokaci ne na neman kusanci da Allah da yin sadaka da saukaka wa jama’a ba wai kuntata musu ba, ya nuna damuwarsa kan cewa duk shekara sai ‘yan kasuwa sun kara farashin kayan masarufi.

Ya nemi ‘yan kasuwan da su taimaki masu azumi ta hanyar daina tsauwala farashi, a maimakon hakan ya jawo hankalin masu hannu da shuni da su rungumi dabi’ar sadaka da ciyarwa a cikin watan na Azumi domin ribantar falalar da watan ke zuwa da su.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button