
Ramadana- Buhari Yayi Kira Ta Musamman Ga Masu Hali
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya al’ummar musulmi a fadin Nigeria da duniya murna dangane da shigowa cikin watan Ramadana wata mai dumbin falala da albarka sai kuma ya bukaci masu hannu da kumbar susa da su taimaka wa mabukata da suke da karamin karfi a cikin al’umma lura da dumbin lada da sada ke da shi a irin wannan watan na Azumi.
A sakonsa na taya murna ga al’ummar musulmin Nijeriya da ma duniya baki daya dauke da sanya hannun hadiminsa Malam Garba Shehu, Buhari ya ce wannan damace mai kyau ga masu kudi da su taimaka wa talakawa domin neman tsira duniya da lafiya.
Har-ila-yau, ya kalubalanci musulmai da su kauce wa ayyukan ashsha a cikin wannan watan da ka iya lalata musu ibadansu, ya jawo hankalin al’umma da a dukufa yin ibada da neman yafiya a wajen Allah madauki domin dacewa da falalar da watan ke zuwa da su.