Labaran Yau

Yadda Ake Hada Miyar Taushe Wato Miyar Gyada Meh Dadi [Updated]

Yadda Ake Miyar Taushe (wato miyar gyada)

Kamar yadda wata daga cikin mabiyin shafinmu na Labaranyau Blog ta bukaci mu muyi bayani dalla dalla kan yadda ake hada miyar miyar gyada saboda tanaso ta birge mijinta idan zai dawo daga tafiya.

Kayan hadin miyan Taushe

Kayan miya
Alaiyahu
Nama
Gyada
Kabewa
Mai (manja ko na gyada)
Maggi Mai dandano
Kayan kanshi irin su Onga da sauransu
Citta da tafarnuwa
Gishiri
Kanwa

Yadda ake hada miyar taushe

Na Farko

DOWNLOAD MP3

A markada ko jajjaga kayan miya. A zuba maggi da gishiri da kanwa kadan.Bayan ya dahu a zuba mai a soya sama sama da manja ko man gyada

Na Biyu

A yanka Kabewa kanana. A wanke nama a hade a Dora a tukunya a zuba gishiri kadan da albasa a rufe ya dahu Amma kar kabewar ta yi laushi lubus

DOWNLOAD ZIP

Na Uku

Idan su kabewar suka dahu zasu hada kansu

Na Hudu

Sai a zuba kayan Miyar akan su kabewar a kara ruwa yadda ake so. A zuba gyada nikakkiya koh dakakkiya

Na Biyar

Idan ya tafasa sai a juya a zuba su Maggi da gishiri.

Na shida

Idan komai ya dahu yanda ake so sai a zuba albasa a juya. A tabbatar komai yaji yanda ake bukata. Sai a zuba alaiyahu. A bashi minti kadan kar a rufe ayi nisa dan zai iya konewa ko ya dahu dayawa, sannan A sauke

Na Bakwai

Aci da Tuwon shinkafa, Masara, semovita ko masa koh sinasir ko funkaso

Idan Hakan Zai Dan Baka Wahala Zaka Iya Yin haka

In zaki hada miyar taushe zaki wanke ki yanka alaiyahu ki ajiyeshi agefe, sai ki yanka kabewa ki dafata ki mitstsika ta ki ajiyeta agefe.

Zaki zuba kayan miyar ki acikin tukunya kizuba mai (manja aka fi amfani da) kiyita juyawa har sai ya soyu sai kisamu ruwan namanki ( wanda kin Tafasa da Albasa ko kayan kamshi irin su tafarnuwa da citta) ki zuba ki tsaida ruwan miyar kizuba kabewar ki kijajjaga da albasa da attarugu .

ki zuba kisa maggi da spices dinki masu dadin d’andano sai ki rufe su, dawo in sun dahu sai ki zuba alayyahun ki kisaka namanki ki rufe in miyar tayi sai ki sauke.

Aci Tuwo lafiya.

Zaki Iya Bibiyan Bayanan Da Ummi Ta Bayar A Cikin Bidiyon Ta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button