Labaran Yau

Sojoji Sunyi Musanyan Wuta Da Yan Ta’adda A Niger Sunyi Nasaran Ceto…

Sojoji sunyi ruwan bindiga da yan ta’adda a jihar Niger, An ceto shanu dubu biyu

Sojojin Najeriya sun kama sama da shanu dubu biyu, bayan sunyi zuban ruwan bindiga da yan ta’adda, a karamar hukumar Mariga wanda keh jihar Niger.

Kafin a karbe shanayen, yan ta’addan sun kai dari biyar daga birnin gwari Na jihar kaduna, wanda an gansu Suna yawo akan babura a kalla guda dari wanda suka shiga kauyuka dayawa a mariga.

DOWNLOAD MP3

Wani mai fada aji a yankin, Adamu warari ya bayyana cewa yan ta’adda Suna shigowa da manyan makamai, basu yi ta’addancin da tsoro koh fargaba.

Shiga suke yi Suna kashe mutane, Suna Kona masallatai da coci, Suna diban kayan matsarufin mutane a gidajen su. Suna tafiya da mata da kuma dabbobin su, Kamin a ce za kai karawa jami’an tsaro.

Adamu Warari yace, yan ta’addaan sun fito ta Birnin-Gwari suka Biyo ta Mariga, sukayi ta kasuwan Garba, wajajen kwantagora,kwimo suka ratsa magadan daji, yungo, argida, zuwa chabadi inda suka kai farmaki suka Saci shanu dari Kamin sojoji suka far musu daga bangi a kwimo.

DOWNLOAD ZIP

Sojojin sama sun bayyana sun samu labarin yan ta addan ne Sai sukayi kokarin bata hanyansu da bamabamai, suka kashe dayawansu.

A nan dai akayi ruwan harsasai har yakai da sojoji biyu suka rasa rayukansu wasu Kuma sun samu rauni.PRnigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button