Labaran Yau

Gwamnonin Kwara, Edo, Ogun, Sun Bada Tallafin Kudi Domin Rage Radadin Tsadar….

Gwamnonin Kwara, Edo, Ogun, Sun Bada Tallafin Kudi Domin Rage Radadin Tsadar Rayuwa Da Cire Tallafin Fetur Ya Jawo

A ranar 29 ga watan Mayu ne shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da kawo karshen tsarin tallafin man fetur a fadin kasar nan gaba daya.

Daukar tallafin man fetur nan take ya haifar da tashin gwauron zabin farashin man fetur, tare da hauhawar farashin kayan abinci, tsadar sufuri da tsadar rayuwa.

A kwanakin baya dai farashin man fetur ya tashi daga matsakaicin Naira 500 zuwa Naira 617 a kowace lita a wasu gidajen man.

Wasu jihohi sun dauki matakan rage tasirin tsadar fetur din ga ma’aikatan su ta hanyoyin da bai fi karfin sub a a gwamnatan ce.

Wasu matakan sun haɗa da shirye-shiryen canja albashi mafi karanci, samar da manyan motocin bas a farashi mai karanci, da biyan haƙƙokin ma’aikatan gwamnati, gami da ƴan fansho.

A watan Yuni ne gwamnatin jihar Kwara ta ba da umarnin rage kwanakin aiki daga biyar zuwa uku don rage tsadar sufuri ga ma’aikatan gwamnati.

A ranar 24 ga watan Yuli, Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, ya amince da tallafin tsabar kudi N10,000 ga kowane ma’aikacin gwamnati a jihar daga watan Yuli.

Abdulrazaq ya ce tallafin kudi zai dore har sai an bullo da sabon mafi karancin albashi.
Gwamnan ya kuma amince da biyan sabbin alawus alawus, da kuma “CONMESS 100% ga masu ba da shawara da likitocin da ke karkashin tsarin albashin gwamnatin Jahar ta Kwara”.
Ya kuma ce za a fara aiwatar da tsarin raba abinci ga marasa galihu lokaci lokaci
EDO

Kamar yadda jihar Kwara, gwamnatin jihar Edo, a ranar 6 ga watan Yuni ta rage wa ma’aikatantanta ranakun aiki daga biyar zuwa uku.

Godwin Obaseki, gwamnan, ya kuma ce jihar na kokarin zurfafa shirin EdoBEST@Home don samar da karin azuzuwa don rage tsadar zirga-zirgar iyaye, malamai da dalibai zuwa makarantu.

Dangane da hauhawar farashin fetur, Obaseki ya ce jihar za ta hada hannu da kamfanonin wutar lantarki don inganta wutar lantarki ga gidaje da kasuwanci.

Gwamnan ya kuma tabbatar wa da ma’aikata cewa gwamnati za ta ci gaba da biyan N40,000 a matsayin mafi karancin albashi da kuma cewa adadin na iya karuwa a nan gaba.
OYO

A wani yunkuri na saukaka wa mazauna garin, Seyi Makinde, gwamnan Oyo, ya ba da umarnin tura karin “Bas din Omituntun” (bas din jigilar jama’a na jihar) don saukaka farashin sufuri.

Makinde ya kuma bayar da umarnin cewa kada a kara kudin motar bas ga mazauna kuma a bar yara ‘yan makaranta da manyan ’yan kasa shiga bas a kan rabin farashin.

Gwamnan ya kuma ce ya kafa kwamitin “domin duba abin da gwamnatin tasa zata iya yi game da karin albashin ma’aikatan gwamnati” OGUN Domin saukakawa mazauna yankin, gwamnatin Ogun ta sanar da biyan N10,000 na tallafin kudi ga daukacin ma’aikatan jihar.

An kuma saka masu karbar fansho a cikin shirin wanda zai fara aiki daga Yuli, na tsawon watanni uku.
Gwamna Dapo Abiodun, ya kuma amince da biyan alawus alawus ga dukkan ma’aikatan lafiya a jihar da kuma wani alawus na musamman ga ma’aikatan gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button