Labaran Yau

Shugaban Kasa Buhari Ya Yarda Da Daga Kidayan Bayan Zaman Da Yayi Da…

Buhari ya amince da daga kidaya

Shugaban kasan Najeriya Muhammadu buhari ya amince da daga kidayan da za ayi wa mutane da gidaje ranan 3 ga watan mayu zuwa 7 ga watan mayu.

Ministan sadarwa da Al’ada Lai Mohammed, ran Asabar yace a Abuja cewa an daga kidayan da za ayi Sai lokacin da gwamnati mai jiran gado ta saka ayi.

A jawabin da ya fitar da sa hannun sa, ministan yace Shugaban kasan ya yarda da daga kidayan bayan zaman da yayi da Majalisan kasa da Shugaban Hukumar kidayan da mukarrabansa.

Ministan, wanda ya rike tagwayen jagoranci na kwamitin bayanin wa jama’a da na kidaya, yace zaman anyi ne a fadar Shugaban kasa Villa a Abuja ran jumma’a.

“Bayan mun yake hukuncin tsayar da kidaya, a zaman an jaddada muhimmancin kidaya bayan shekara goma sha bakwai daya gabata.

“Hakan zai taimaka wajen samo yawan adadin mutane da gidaje wanda zai jawo cimma burin mu na kawo cigaba a kasan da kuma inganta rayuwar mutane”, Ministan yafi hakan kalaman Shugaban kasan yayi.

A bayanin ministan, shugaban kasa ya yabi aikin da akayi wajen aiwatar da kudirin kidayan mutane da gidaje.

Ya ce Shugaban kasan ya yabi daukan ma’aikatan da akayi da horaswa da wanda zasu dau nauyin yanan gizo da kuma dakunan komputa.

Mohammed ya bayyana cewa Shugaban kasan ya yabi matakan da aka dauka wajen yin kidaya mai inganci.

Yace an sako yawan takanolaji dan samu ayi kidaya wanda zata bada abinda ake nema dan ya taimaka wajen kawo maslaha a kidayoyin da za ayi a gaba.

Ministan ya kara da cewa Shugaban kasa ya baiwa Hukumar kidaya karfin gwiwa na ci gaba da tsare tsaren kidayan koh nunuwar aikin zaisa gwamnati da zata shigo tayi kidayan nan take dan cimma burin mu.

Wanda suka halarci zaman sun hada da, ministan Adalci Abubakar Malami, ministan kudade da tsare tsare Zainab Ahmed dashi kanshi Lai muhammed.
Da Clem Agba, Ministan jiha na tsare tsaren kasa da Sakataren gwamnatin kasa Boss Mustapha.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button