Labaran Yau

Gwamna Yusuf Ya Sa An Rusa Shataletale A Kano

Gwamna Yusuf Ya Sa An Rusa Shataletale a Kano

Gwamnatin Jihar kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bada umarnin rushe zagaye na tumbin giwa wanda ke hanyar Jiha wajen gidan gwamnati.

Zanen zagaye na shataletalen ya kasance madubi ne wa jihar kano, media da yan wasan kwaikwayo a shekarun baya da suka wuce.

Daya daga cikin aikin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

An rusa zagayen a safiyar laraba dan cigaba da rushe gine ginen da akayi ba bisa doka ba. Wanda hakan yana har gitsa tsarin Jihar.

Zagaye Mai tarihin, ya samu gyara ne karkashin gwamnatin da ta gabata wanda an kashe kudi akai har naira miliyan 160 a shekarar 2017.

Sabuwar gwamnati a safiyar lahadi ta rusa shaguna wanda aka gina a jikin filin wasa na Sani Abacha na kofar mata, GSS Kofar Nasarawa da kuma gine ginen GGSS Dukawuya, Goron Dutse.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button