`Yan-A-Mutun Buhari Sun Zama Marayu A APC Cewar Shehu Sani
Tsohon sanata mai wakiltar kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, yayi ba’a wa masoyan tsohon shugaban kasa Muhammadu buhari, cewa sun zama marayu.
DailyNigeria ta bada rahoton cewa Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu, ranar lahadi ya ajiye aikin sa saboda juya masa baya da akayi daga makusanta na shugaban kasa Bola Tinubu.
Shehu Sani ya wallafa a shafin sa na Twitter, cewa Tinubu yana kau da masoyan buhari daga jam’iyyar.
“Yan buhariyya sun zama marayu, Ana fitar dasu ko yaya” sanatan ya fada.
Daily Nigeria ta bada rahoton cewa Adamu shine wanda Buhari yake so, shi yaci zaben shugabancin jam’iyyar wanda akayi a watan Maris a shekarar 2022.
A farko kamin ayi zaben Firamare na shugaban kasa, tsohon gwamnan Jihar Nasarawa ya bayyana Tsohon shugaban Majalisan dattawa Ahmed Lawan a matsayin dan takarar APC.
Amma Fadar shugaban kasa da gwamnoni da suka ci zabe karkashin jam’iyyar APC sun kori maganar Adamu Sai suka bada Goyon baya Tinubu.