Labaran Yau

Fabregas Ya Zama Sabon Kocin Kwallon Sawu Na Como B Dake Kasar…

Fabregas Ya Zama Sabon Kocin Kwallon Sawu Na Como B Dake Italiya

Biyo bayan ritaya da tsohon Dan wasan andalus din yayi a yau asabar ya sanar a shafinsa na tuwita Akan cewar ya zama koci. “Wannan shine lokacin da yafi dacewa na fara aikin horaswa“. A cewar Cesc Fabregas din.

Dan wasan yana cikin yan wasa mafi nasara a tarihin kasar andalus din. Ya ci kofin duniya da kasarsa sannan yaci kofin zakarun nahiyar turai da Chelsea dake ingila.

Ya fara bugawa a Barcelona kafin nan ya koma kungiyar arsenal dake landan a ingila. Cesc yana cikin kadan daga cikin yan wasan da suka bugawa Chelsea da arsenal wasa.

DOWNLOAD MP3

Sauran nasarorin da Cesc din ya samu sun hada da cin kofin Europa league guda daya, kofin kasashen turai guda biyu da kuma La Liga da tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona. Muna yi masa fatan nasara a rayuwarsa ta horarwa a italiya.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button